Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Zabi Ghana Da Wasu Kasashen Afirka 3 A Majalisar Kare Hakkin Dan Adam


Taron UNGA
Taron UNGA

Majalisar Dinkin Duniya ta zabi kasar Ghana da wasu kasashen Afirka uku a cikin sabbin mambobi 15 da za su kasance a kwamitin kare hakkin bil adama, ta hanyar zaben sirri. Wannan kwamitin na Majalisar na da alhakin kare duk wani hakkin dan Adam a duniya.

Ambasada Dennis Francis na kasar Trinidad da Tobago kuma shugaban Majalisar ne ya bayyana sunayen kasashen da aka zaba, bayan da aka kada kuri'un sirrin.

Kasashen su ne Albaniya, Brazil, Balgariya, Burundi, China, Côte d’Ivoire, Cuba, Jamhuriyar Dominika, Faransa, Ghana, Indonesiya, Japan, Kuwait, Malawi da kuma Netherlands.

Yace "wadannan kasashen ne aka zaba, kuma za su yi aiki na shekaru uku daga ranar 1 ga watan Janairun 2024."

An kirkiro kwamitin ne a watan Maris na shekarar 2006, a matsayin babbar hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da hakkin dan Adam.

Kwamitin na kunshe ne da mambobin kasashe 47 da ake zabarsu bisa ga tsarin shiyyoyi biyar, inda nahiyar Afirka take da kujeru 13; yankin Pasifik na Asiya kujeru 13; Gabashin Turai 6; Latin Amurka da Karebiya, kujeru 8; sannan sai Yammacin Turai da sauran Jihohi da ke da kujeru 7.

Alhaji Abdul-Rahman Gomda, editan jaridar Daily Guide da ke Accra yace zaben da aka yi wa Ghana na nuni da cewa duniya ta amince da kokarin da kasar ke yi wajen kare hakkin bil adama.

Ya ce"Majalisa da duniya baki daya na nuni da cewa sun amince da inda Ghana ta kai wajen kare ‘yancin bil adama, idan muka dubi inda muka fito wasu shekarun da suka wuce, tun zamanin mulkin (soji) AFRC, PNDC da sauransu, mun ga abubuwa da yawa da ba su dace ba. Amma, da dimokradiya ta samu zama a kasar, abubuwa da yawa sun canja. Don haka, abin murna ne gare mu ‘yan Ghana."

Kasar Malawi ce ke kan gaba a kasashen Afirka, da kuri'u (182), sai Cote d'Ivoire (181), Ghana (179), Burundi (168), sai Najeriya na da (3).

Malam Issah Abdul Salam, mai shirhi kan harkokin siyasa da al’amuran yau da kullum kuma sakataren jam’iyar CPP na yankin Ashanti yace lallai kasar Ghana na kokari wajen kare hakkin bil adama, kuma yana fatan hakan ya dawwama, kasar ta wuce inda ta kai yanzu.

Ya kara da cewa "haka kuma muna fatan gwamnati za ta kara kaimi wajen fadada kare hakkokin bil adama, yadda zaben da za'a yi nan gaba, Ghana za ta kasance na farko a nahiyar Afirka don kara daga matsayin kasar a fuskar duniya."

Sabbin kasashen 15 din da aka zaba, za su hadu da sauran kasashe 32 da suka hada da, Amurka, Sudan, Jamus, Bangladesh, Argentina, Kazakhstan Maldives, Eritrea, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da sauransu, a ranar 1 ga watan Janairun 2024 don su fara wa’adin shekaru uku na aikin kiyaye hakkin bil adama na duniya.

Saurari rahoton Idris Abdallah:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG