Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Nemi Karin Tallafin Biliyoyin Daloli Na Yaki Da Tasirin COVID-19


Majalisar Dinkin Duniya ta sake yin kiran neman tallafin biliyoyin daloli sakamakon coronavirus, tana cewa hakan ya zama wajibi domin kare rayukan miliyoyin mutane da kuma taimakawa a magance yaduwar cutar a kasashe marasa karfi.

Hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta fada yau Alhamis cewa, ba’a tsammanin za a kai kokoluwa a annobar COVID-19 a kasashe matalauta a duniya, har sai zuwa nan da wata uku ko shida masu zuwa, amma tuni aka fara samun rashin aikin yi da karancin kudaden shiga, da kuma rashin samun isassun kayan abinci, a yayin da yara suke gararamba ba tare da rigakafi ba.

Tun da farko hukumar ta bukaci tallafin dalar Amurka biliyan biyu, to amma kuma a yau Alhamis ta ce, tana bukatar adadin da ya kai dala biliyan shida da miliyan 700.

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta MDD, Chief Mark Lowcock, ya ce dan ba'a taimakawa mutanen da suke cikin tsananin talauci ba, musamman mata da ‘yan mata da wasu rukunin da ke cikin hadari a yayin yaki da annobar, to kuwa "za mu yi fama da ragowar cutar a shekaru masu zuwa. Wannan zai fi radadi da kuma tsada ga kowa".

Karin neman taimakon ya zo ne sakamakon karin kasashe tara masu rauni, wato kasashen Benin da Djibouti da Liberia da Mozombique da Pakistan da Philippines da Sierra Leone da Togo da kuma Zimbabwe.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG