Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CORONAVIRUS: Watsi Da Dokokin Hana Yaduwar Annobar A Iran


Tashar Talabijin ta kasar Iran ta nuna hotunan yadda masu ibada suke yin watsi da umarnin gwamnati na sanya takunkumin rufe fuska a masallatan da hukumin suka bude a biranen da ake zaton an ci karfin yaki da cutar coronavirus.

Wani rahoto da tashar talabijin ta IRIB dake kudu maso gabashin lardin Kerman kawar na Iran ta yada hotunan a jiya Talata, ya nuna maza da mata suna Sallah ba tare da sanya abin rufe fuska ba a manyan biranen Lardi uku, da suka hada da Roudbar, Kahnouj da Manoojan.

Rahoton ya nuna Masallaci daya tilo ne a gundumar Rigan inda duk masu ibada suke sanye da abin kariyar fuskar.

Musamman kuma, mazan sanye da abin kariyar a rigan, sun bada tazarar kimanin rabin mita tsakaninsu, cikin mutumta wani umarnin gwmanti na yin nesa-nesa da juna a yayin Sallah. Bisa ka’idar Musulunci dai, musulmai na tsayuwa kafada da kafada da juna ne a yayin Sallah cikin jam’i.

A wata sanarwar da ya bayar a ranar Lahadi, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, yayi umarni da a bude Masalatai daga ranar Litinin a gundumomi 132 inda ake zaton barazanar cutar ta yi kasa.

Sanya abin kariyar fuska da yin nesa-nesa da juna na daga cikin abubuwan kiyayewa da kuma takaita lokacin da mutune zasu yi a cikin masalatai zuwa rabin sa’a.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG