Majalisar Dinkin Duniya na shirin kaddamar da wani asusun neman tallafin kudaden da za a yi amfani da su wajen tallafawa miliyoyin mutanen da rikicin Boko Haram ya rutsa da su a arewa maso gabashin Najeriya.
Daga cikin wadanda za a tallafawa har da dubban daruruwan ‘yan gudun hijira da suka tsallaka zuwa kasashen da ke makwabtaka da Najeriyar, domin neman mafaka.
Akalla Dala miliyan 983, asusun tallafin zai nema, inda za a yi amfani da Dala miliyan 848 daga cikin kudin wajen tallafawa mutum miliyan 6.2 da suka tagayyara sanadiyar rikicin Boko Haram, a jihohin Borno, Adamawa da Yobe, wato jihohin da rikicin ya fi kamari.
Kusan shekara goma aka kwashe fafatawa tsakanin mayakan kungiyar ta Boko Haram da gwamnatin Najeriyar.
Kakakin ofishin da ke kula da ayyukan agaji na Majalisar Dinkin Duniya, Jens Laerke, ya ce, rikice-rikicen da suka taso a ‘yan kwanakin nan, sun raba fararen hula sama da dubu 80 da muhallansu.
“A jimillance, mutum miliyan 1 da dari 8 aka raba da muhallansu a yankin arewa maso gabashin Najeriya, sanadiyar wannan rikici, wanda ya haddasa cin zarafin fararen hula ta hanyar kisa, fyade da garkuwa da mutane.” Inji Laerke.
Ana sa ran za a kwashe shekara uku wajen aiwatar da wannan tsarin tallafi ta hanyar amfani da kudaden da za a tara.
Facebook Forum