Shugabannin duniyar sun tabbatar da wannan tsarin kiwon lafiya ga kowa ne a wani taron gefen taron kolin Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya tattara maharalarta da suka hada da babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, da shugaban taron kolin Majalisar Dinkin Duniya na 74 Tijjani Muhammad Bande, da babban darektan hukumar kiwon lafiyar Majalisar Dinkin Duniya ta WHO Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus, da kuma wakilan gwamnatoci, da na kungiyoyi masu zaman kansu, da sauransu.
Antonio Guterres ya kwatanta wannan sanarwa a matsayin wata gagarumar nasara ce da zata samar da ci gaba shekaru goma masu zuwa, a yaki da cututtuka da ake iya dauka kamar cutar SIDA, da tarin fuka, da Malariya, yayin da ake kuma magance cututtukan da ake iya dauka ta wannan hanyar samar da kiwon lafiya a mataki na farko mai inganci.
Guterres yace wannan sanarwar siyasar a kan tsarin kiwon lafiya ta bayyana muhimmancin samar da ‘yancin kiwon lafiyar jima’i, da haifuwa ga kowa. Yace tana da kuma muhimmanci ga kare walwala, da mutuncin mata da ‘yan mata.
A nasa bangare babban Darektan WHO Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus, yace suna kira ga duk kasashe da su kara zuba jari a kan samar da kiwon lafiya, matakin farko da akalla kashi daya cikin dari na dukiyar kasa, ta hanyar kara kasafi ko sauya mazaunin tsarin kiwon lafiya ko kuma biyu duka.
Yace hukumar kiwon lafiya ta WHO ta kiyasta wannan jari na fannin lafiya zai ceto rayuka kimanin mutane miliyan 60 a duk shekara, kana ya kara yawan shekarun al’umma da kashi 3.7 nan da shekarar 2030.
A saurari cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Baba Makeri.
Facebook Forum