Shugaban kungiyoyin Da'awa na kasa a Najeriya, Sheikh Mohammed Lawal Mai-Doki Sokkoto, wanda yayi magana a babban taron da'awa da suka yi a Minna, fadar jahar Nija, yace yadda ake amfani da kafafen sada zumunta wajen fadin abunda kowa ya ga dama ba tareda kuma an hukunta masu yi ba, sakamakon haka shine jefa kasa cikin yaki.
Shiekh Mohammed yace, mutane su duba abunda yake faruwa a Syria, da Iraqi, da Libya,shin irin abunda suke fata suga yana faruwa kenan a Najeriya?
A tasa gudumawa, wani malami a sashen Larabci a kolejin Ilmi ta jahar Nija dake Minna Dr. Abubakar Kawu-Hassan, yace rashin tilasta ilmin addini akan 'yan kasa, yana daga cikin dalilai da suke haddasa kwararar dalibai zuwa cikin kungiyoyin ta'addanci kamar Boko Haram, da kuma ISIS. Yace saboda dagewa dalibai su koyi kimiyya da fasaha kadai,bayan sun sami ilmin, amma babu na addini, yanzu, sun juya suna amfani da ilmin kimiyyar wajen kerawa 'yan ta'adda makamai.
A cikin watan kasida da ya gabatar, Farfessa Isah Mohammed Mai-shanu, na jami'ar Usman Dan Fodio dake Sokkoto, yayi magana ne kan zakal-kalewa wajen yin da'awa.Yace zakalkalewa ko wuce makadi da rawa, shine ya haifarda kungiyoyi irin su Boko Haram, wadanda suke aikata abubuawa sabanin abunda addini Islama ya fada.
Haka nan Farfessan yace yin barace barace, inda ake zuba yara kan tituna da suna neman ilmin addini, ba addini Islama bane.
Ga karin bayanin rahoton da Mustapha Batsari ya aiko mana.
Facebook Forum