Kasar Sri Lanka ta katse hanyoyin amfani da kafafen sada zumunta don dakile yaduwar tashe-tashen hankula kan al’ummar Musulmi tsiraru, yayin da daukacin wannan tsibirar kasa ta kudancin Asiya, ke cigaba da kasancewa karkashin dokar ta baci.
Shugaba Maithripala Sirisena ya kafa dokar ta bacin ne jiya talata, kwana guda bayan da cincirindon masu bore na kabilar Sinhalese da ke bin addinin Buddah su ka kai hare-hare kan masallatai da dama, da kuma wuraren kasuwancin al’ummar Musulmi a yankin tsakiyar gundumar Kandy. Jiya talata ‘yan kwana-kwana sun gano gawar wani matashi Musulmi wanda ya makale lokacin da wuta ta kama wani karamin kantin mahaifinsa.
Tashen hankalin ya samo asali ne ranar Asabar, lokacin da wani direba dan kabilar Sinhalese ya yi fada da wasu matasa Musulmi a Kandy. Washe gari direban ya mutu sanadiyyar raunukan da ya ji.
Facebook Forum