Har yanzu ba a ga yara ‘yan makaranta fiye da 300 ba a Najeriya, kwana hudu da wasu ‘yan bindiga suka sace dalibai a makarantar sakandire dake Kankara, yayin da fargaba ke karuwa.
‘Yan bindiga na Boko Haram sun yi ikirarin su ne ke da alhakin sace daliban daga makarantarsu a Katsina dake arewacin Najeriya a makon jiya, a daya daga cikin hare-hare mafiya girma a shekaru.
Yaron Marwa Hamza Kankara dan shekara 14 ya na daga cikin wadanda aka sace.
Marwa ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewa: “Yau kwana hudu kenan da muke zuwa makarantar, kuma ba ma komawa gida sai karfe 6 na yamma. Ba ma iya cin abinci, ba ma iya barci saboda bacewar ‘ya’yanmu.”
Gwamnati ta na tattaunawa da maharan domin sako daliban, acewar Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
“Wadanda suka yi garkuwa da daliban sun tuntubi gwamnati, kuma ana tattaunawa da su a game da dawo da daliban cikin koshin lafiya, acewar Garba Shehu a shafin Twitter yayin tattaunawa da Gwamnan Katsina Aminu Masari.
Babu wani jami’i da ya tabbatar da ko da kungiyar Boko Haram ake tattaunawar.
Karin bayani akan: Boko Haram, sojoji, da jihar Katsina.
Labarai masu alaka
Zangon shirye-shirye
-
Nuwamba 04, 2024
Yaushe Ne Bakon Haure Yake Samun Damar Kada Kuri’a A Zaben Amurka?