Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Kwankwaso Yayi Kira ga Gwamnatin Tarayya ta Kawo Karshen Tashe Tashen Hankula


Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso.
Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso.

Gwamna Kwankwaso yace al'amarin yanzu ya dami kowa in banda wadanda hakkin kawo karshen rikicin ya wajaba akansu.

Ranar Jumma'a ce wani dan kunar bakin wake ya halaka kansa tareda wasu mutane biyar a wani gidan mai da bashi da nisa da babbar tashar kamfanin mai na Najeriya watau NNPC.

Da yake amsa tambayoyi a wata hira da Sashen Hausa na Muriyar Amurka, bayan harin da aka kai kan wani kolejin ilmi har aka halaka mutane masu yawa cikin watan Yuli, Gwamna Kwanso yace, hare hare ya zama kusan ruwan dare a Najeriya musamman daga arewacin kasar.

Daga nan yayi kira ga wadanda nauyin kawo karshen wannan fitina ta rataya a wuyansu suyi bakin iyawarsu ciki harda gudanar da shawarwari da wadanda suke tada kayar baya, wajen ganin an magance wannan rigima.

Gwamna Kwankwaso ya kuma yi magana kan irin nasarori da gwamnatinsa ta samu a fagen imi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG