A shirin matasa da siyasa a yau, DandalinVOA ya sami bakunci Abubakar Abdullahi Kana Baru, shugaban kungiyar Salihiyya nasiha, wanda ya ce a yanzu matasa a wannan zabe mai zuwa zasu kauracewa ta da zaune tsaye.
Matashin ya bayyana cewa zaton nan da mutane su ke yi a da a lokacin zabe, hakan ba zai faru ba a wannan karon, domin kuwa a yanzu matasa sun farga, a zabe mai karatowa zasu nisanta kan su da tashin hankali.
Ya kuna ce matasa mussaman wadanda suke daba a da, a yanzu kam duhu ne ya ke dukan duhu, sai dai su karbe kudaden 'yan siyasa masu so su ta da zaune tsaye. A maimakon hakan a yanzu matasa zasu fi maida hankali wajen zaben cancanta.
Abubakar ya kara da cewa a yanzu sakamakon yawan wayar da kan matasa, sun gane muhimmancin zaben nagari da nuna musu makomar wasu 'yan dabar da suka shiga hannun hukuma da yadda 'yan siyasar suka kauracewa musu a gidajen kurkuku.
A saboda haka yanzu matasa sun canza salon karbar kudade daga wajen manyan 'yan siyasa tare da yin buris da bukatunsu na daba, ko kuma su karbe kudaden sannan su bukaci 'yan siyasar da su turo ‘yayensu domin su aiwatar da abin da suke bukata.
Abubakar ya ja hankalin matasa da su jajirce wajen kishin kasar su, tare da tabbatar da cewa sun yi zaben cancanta domin ci gaban kasa da su kansu matasan.
Facebook Forum