Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa a Bauchi Sun Mika Makaman Boko Haram Ga Hukuma


Sojoji Najeriya kusa da Maiduguri,
Sojoji Najeriya kusa da Maiduguri,

Matasan garinn Tafawa Balewa a jihar Bauchi sun mika kayan yaki wanda ‘yan kungiyar boko haram suka watsar a bayan da aka fafata a lokacin da yan kungiyar suka kawo hari a garin na Tafawa Balewan da basu samu nasara ba.

Kayan yakin dai sun hada da bindigar kakkabo jiragen sama dakuma wasu kananan bindigogi, matasan sun mika kayan ne ga hannun shugaban STF manjo janar DD Etetei a garin na tafawa balewa wanda ya bayyana godiya da halin kishin zuci da na son kasa da matasan suka nuna.

Kakakin STF kaftin Iweha yayi karin bayanin cewar "a kwai makamai da dama wadanda matasan suka mika mana, kuma zamu cigaba da sa ido da kara cigaba da bincike. Za a kai kayayyakin inda ya kamata a ajiye su kuma bayan matsalolin sun lafa, za a nuna wa jama'a duk abubuwan da aka amso daga hannun 'yan ta'adda."

Shima hakimin Bagwaro Malam Sarauta Damina ya tofa albarkacin bakin sa cewar suna matukar farin ciki da wannan kokari da matasan suka yi, kuma ya kara da cewa sarkin garin ya basu umurnin cewa duk lokacin da aka sami wasu abubuwa makamantan wadannan su yi maza maza su mika su ga hukuma.

Daga karshe sakataren matasan garin Tafawa Balewa Mr Ezra John yayi karin bayanin cewa suna masu godiya ga Allah da ya basu damar samun yin galaba kan 'yan kungiyar. kuma ya bayyana cewar za su cigaba da sadaukar da rayukan su domin bada kariya ga kasar su.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG