Magoya bayan jam'iyyar NDP sun ce kwarjinin da matar Rawlings ke dashi ka iya zama babbar kalubale ga shugaban kasar na yanzu John Dramani Mahama a zaben shugaban kasa da za'a yi ranar 7 ga watan Nuwamban wannan shekarar.
An zabi ita matar Jerry Rawlings din ce a babban taron wakilan jam'iyyar da suka gudanar ranar Asabar da ta gabata a Accra babban birnin kasar ta Ghana.
Sakataren National Democratic Party Mohammed Frimpong yace Agyeman-Rawlings ita ce 'yar takarar da ta fi dacewa wajen kawo canjin da 'yan kasar Ghana ke nema ruwa ajallo.
"Duk 'yan kasar suna son ta dawo faggen siyasa domin ta ba 'yan Ghana abun da ta fi sani ta kuma kure a kai kamar iya tattara goyon bayan jama'a da taimakawa mata su samu dogaro da kai da dai sauransu. Dalili ke nan da jam'iyyar NDP da dimbin magoya bayanta a duk fadin kasar suka amince baki daya su tsayar da ita a matasyin 'yar takarar shugaban kasa", inji Frimpong.
Tsohon shugaban kasar Jerry John Rawlings wanda kuma shi ne ya kafa jam'iyyar dake mulki yanzu, wato National Democratic Congress ko NDC ya nuna goyon bayanshi ga matarsa kafin jam'iyyar NDP ta tsayar da ita 'yar takarar shugaban kasa.
Yanzu abun da ake jira a gani shi ne ko tsohon shugaban zai goyi bayan matarsa ta kara da shugaba John Dramani Mahama na jam'iyyar NDC mai mulki, jam'iyyar da shi Jerry Rawlings ya kafa.