Wannan kiran ya fito ne bayan kungiyar ta yi gangami tare da wasu kungiyoyin fararen hula dana ‘yan adawa a yankin ‘yan kabilar Ashanti da ke birnin Kumasi a jiya Laraba. Shugaban kungiyar David Asante yace, sun shirya yin zanga-zanga a fadin kasar don matsawa hukumar zaben tattaro sahihin kundin sunayen masu zaben.
Yace abin takaici ne ganin yadda hukumar bata yin amfani da rahoton kwamitin da ta kafa bata jin koken jama’a game da rashin sahihancin kundin sunayen masu zaben kasar da aka yi amfani da shi a zabeukan baya. Asante yace ba kuma wata maganar zama teburin yarjejeniyar janye wannan batu da suka faro.
Ya bayyana cewa, makasudin gangamin da za su gabatar a kasar shine, don tabbatar da cewa hukumar zaben kasar ta yi abinda ya kamata na ganin an aiwatar da sahihin zaben a zabukan kasar da ke tafe a watan 11 idan Allah ya kaimu. Saboda haka wannan na nuna cewa suna nan suna lura da al’amuran zabukan kasar.