Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci sansanin da aka tsugunar da mutanen da ambaliyar ruwa ta kwashewa gidaje a jihar Neja dake arewacin Najeriya. Kimanin mutane 500 aka tara a wata makarantar firamare a garin Zungeru dake karamar hukumar Wushishi a sakamakon rasa gidajensu a garuruwan Gungu, Aboki da kuma Rafin gora.
Ya tabbatar da cewa gwamnati zatayi iya bakin kokarin ta don ganin an taimakawa wadanda abin ya shafa
Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello yace a yanzu haka akwai garuruwa kimanin 130 da ambaliyar tayi wa illa don haka jihar zata bada gudunmawa ga wanda abin ya shafa.
Ga Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani..
Facebook Forum