Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siyasar Jihar Adamawa Ta Dauki Sabon Salo


ADAMAWA: Gwamna da mataimakinsa
ADAMAWA: Gwamna da mataimakinsa

Wasu kusoshin jam’iyar ne dake tare da bangaren su Murtala Nyako,Nuhu Ribadu,Engr Markus Gundiri, da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachur David Lawal, suka garzaya Abuja domin mika kukarsu na a sauke shugabanin jam’iyar na jihar, biyo bayan kalaman da shugaban jam’iyar Ibrahim Bilal yayi na cewa su ba wani dan takarar gwamna da suka sani sai gwamnan jihar Sen.Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla.

To ko me yayi zafi haka? Mr Adamu Kamale, dan majalisar wakilai yace, muddin uwar jam’iyar ta rusa shugabanin jam’iyar, to fa labudda zasu sauya sheka su da sauran magoya bayan gwamnan zuwa wata jam’iya.

Wannan takaddamar dai na ko zuwa ne, yayin da shugabanin jam’iyar ta APC ke lashe aman da suka yi tun farko, inda suka fitar da wata sanarwar gaggawa domin fayyace matsayin game da yan takarar gwamnan.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz..

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG