Sarki Abdallah na Jordan ya bayyana damuwarsa game da shawarar Amurka ta yanke na amincewa birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila. Sarkin ya baiyana wannan damuwa yayin da yake tattaunawa da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence.
Yayin da yada da zango na biyu a ziyarar kwanaki hudu a yankin Gabas ta Tsakiya, Pence ya fada cewa kasashen biyu sun sabawa juna tare da fahimtar juna a kan wannan shawara mai tsarkakiya da Amurka ta sanar a watan da ya gabata.
Ya ce galibi abokai zasu iya saba ma juna, kuma su fahimci juna a batun birnin Kudus. Mun yarda akwai bukatar duk bangarorin su koma a kan teburin tattaunawa. Ina fatan na nua masa sha’warmu ta sake tada inji din shirin samun zaman lafiya, inji Pence yayin da yake ganawa da manema labarai.
Sarkin Jordan ya fada mataimakin shugaban Amurka cewa, hanya daya na magance rikicin Isra’ila da Falasdinu, itace raba yankin biyu, don haka gabashin birnin Kudus ya zama babban birnin Falasdinu a nan gaba.
Kafin ya isa Jordan, Pence ya fara yada zango ne a Misira inda yayi alkawarin Amurka zata ci gaba da taimaka mata wurin yaki da ta’addanci.
Ziyarar Pence a Gabas ta Tsakiya itace ziyara da wani babban jami’in Amurka ya kai a yankin tun bayan da shugaba Donald Trump ya sanar Amurka zata dauki birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila a watan Disemba da ya gabata.
Facebook Forum