Dubbanjama'a suna cire ‘ya’yansu daga makarantun dake yankin da ake amfani da harshen Ingilishi na kasar Kamaru, bayan da 'yan aware suka kai hari suka kuma raunata mutane da dama a makarantunsu. Masu fafutukar neman ‘yancin yankunan dake amfani da harshen Ingilishi na kasar Kamaru, sun gargadi iyaye kada su kai ‘ya’yansu makaranta, tare da jadada cewa, ba zasu iya bada tabbacin kare lafiyarsu ba.
Iyaye da dama sun janye ‘ya’yansu daga makarantar kwalejin St Joseph dake da kimamin dalibai dari biyar, bayanda mayaka suka kai hari ranar lahadi da dare. Makarantu da dama a yankin sun shawarci iyaye su maida ‘ya’yansu gida.
A kalla makarantu saba’in aka kona tunda aka fara tashin hankali a yankunan da ake amfani da harshen ingilishin a shekara ta dubu biyu da goma sha shida, lokacin da malamai da lauyoyi suka yi zanga zangar nuna rashin gamsuwa da yadda ake yawan bada karfi kan harshen Faransanci a kasar da ake amfani da harsuna biyu a hukumance.
Facebook Forum