Gwamnatin jihar Nejan tace ta dauki matakin hana Malam Muhammad Bin Muhammad daga yin wa’azi da kuma rufe makarantunsa dake garin Suleja saboda zarginsa da yada manufofi irin na kungiyar Boko Haram.
A ’yan kwanakin nan dai wa’azin wannan malami ya karade kafafen sadarwa na zamani inda a cikin karatun yake amfani da wasu kalmomi masu ta da hankali a kan wasu malaman addinin Musulunci dake Najeriya.
Dr. Umar Faruk Abdullahi babban daraktan Ma’aikatar Kula da Harkokin Addinai ta jihar Neja ya ce da irin wadannan kalamai da kuma da’awarsa na cewa yin zaben dimokradiyya haramun ne a addinin Musulunci, ya sa gwamnatin jihar Neja yanke hukuncin taka masa burki domin gudun tada husuma a tsakanin Al’umma.
Masu kare hakkin ‘dan adam a Najeriya sun ce duk da sun goyi bayan matakin gwamnatin jihar a kan matakin dakatar da wannan malami daga yin wa’azi, amma za su sanya idanu a kan kare masa hakki a matsayinsa na ‘dan adam.
Kwamred Abubakar Abdullahi shugaban kungiyar Kare Hakkin ‘Dan Adam a jihar ya ce kalaman da malamin ke amfani da su za su iya kawo wata fitina.
Suma dai a bangaren Malamai sun ce suna goyon bayan matakin gwamnati, sai dai Sheik Nasiru Hanza daya daga cikin malaman masu wa’azi a Najeriya ya ce gwamnatin jihar ta dan dakata kafin a kai ga daukar wannan mataki.
Azantawa da manema labarai Malam Muhammad Bin Muhammad ya ce ba shi da manufofin kungiyar Boko Haram domin kuwa shima ya yi karatun Bokon.
Abaya dai gwamnatin jihar Nejan ta dauki irin wannan mataki na dakatar da Sheik Ahmed Murshid daga yin wa’azi a karamar hukumar Bida saboda zargin kokarin tayar da hankalin jama’a,
Haka zalika a shekara ta 2009 Gwamnatin jihar Nejan ta kori Shiek Bashir Ahmed tare da magoya bayansa su kimanin 3000 daga wani gari da suka kafa mai suna Darul-Islam a karamar hukumar Mokwa, shima saboda dalilai na bijirewa gwamnati da kuma yada wasu akidu masu kama da na kungiyar ta Boko Haram.
Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:
Dandalin Mu Tattauna