Masoya kwallon kafa a fadin duniya su na cike da doki a yayin da ake shirin fara buga gasar cin kofin kwallon kafar duniya gobe jumma’a a kasar Afirka ta Kudu. Da alamun wannan doki ya fi fitowa fili a kasar ta Afirka ta Kudu, wadda ita ce kasar Afirka ta farko da zata taba daukar nauyin gudanar da wannan gasa.
Za a bude wannan gasa ta tsawon wata guda, kuma ta kasashe 32, da karawar farko a tsakanin Afirka ta Kudu da kasar Mexico a filin wasa na Soccer City wanda aka yi masa kwaskwarima dake birnin Johannesburg. Anan sa ran cewa shugaban Afirka ta Kudu na farko bayan mulkin wariyar launin fata, Nelson Mandela mai shekaru 91 da haihuwa, zai halarci bukin bude gasar na wani dan lokaci a gobe jumma’a.
A bayan Afirka ta Kudu, kasashen Afirka su shida ne suka samu shiga cikin gasar cin kofin duniyar a wannan karon. Kasashen su ne Najeriya, Ghana, Kamaru, Ivory Coast, Masar da kuma Aljeriya. Afirka ta Kudu da ma tana cikin gasar a matsayinta na mai masaukin baki.
Italiya tana halartar wannan gasa a zaman kasar dake rike da kofin, amma kuma kasar Spain, wadda ita ce zakarar nahiyar Turai a yanzu, ita ce aka fi karfafa cewa tana iya lashe wannan kofi a bana.