Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kano: Majalisar Dokoki Ta Amince Da Kudurin Karin Masarautu


Majalisar dokokin jahar Kano ta amince da nada karin sarakunan yanka masu daraja ta daya guda hudu a jahar.

Majalisar dokoki ta jahar Kano ta amince da nada karin Sarakunan yanka, masu daraja ta daya har guda hudu a jihar ta Kano, bayan ta kammala aikin gyarar dokar kula da nadi da aikace-aikacen sarakuna a jahar.

Kakakin majalisar dokokin Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ya jaddada amincewar wakilan majalisar, dangane da kwaskwarimar da suka yi wa dokar nadin sarakuna da aikace aikacen su a jahar.

Gabanin haka sai da ‘yan majalisar suka yi wa daftarin kudurin karatu na biyu da na uku.

Hon. Baffa Babba Dan Agundi, shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin ta Kano, ya fayyace kunshin dokar a ganawar da ya yi da ‘yan jarida.

Yayin da ake tsaka da mahawara akan daftarin dokar, dan majalisa mai wakiltar mazabar Danbatta Hafizu Sani Maidaji, ya fice daga zauren majalisar.

Baya ga dan majalisar ta Danbatta wakilai shida na jam’iyyar PDP a majalisar sun kaurace wa zaman majalisar na jiya da yau, domin nuna adawarsu da yunkurin kirkiro masarautun.

Da wannan ci gaba da aka samu, jahar Kano ta nada masarautu biyar kenan, wadanda suka hada da masarautar Kano, wadda ta kunshi kananan hukumomi goma, wato Tarauni da Dala, Nasarawa, Fagge, Gwale, Kumbotso, Ungogo, Dawakin kudu, da Minjibir.

Sai masarautar Rano mai kananan hukumomin Rano, Bunkure, Kibiya, Takai, Sumaila, Kura, Doguwa, T/wada, Kiru, da Bebeji.

Yayin da masarautar Gaya keda kananan hukumomi takwas, da suka hada da Gaya, Ajingi, Albasu, Wudil, Garko, Warawa, Gezawa, da Gabasawa.

Ita kuwa masarautar Karaye nada kananan hukumomi bakwai ne, wato karamar hukumar Karaye, Rogo, Gwarzo, Kabo, Rimin Gado, Madobi, da Garunmalam.

Sai masarauta ta biyar, wato masarautar Bichi, wadda ke da kananan hukumomi tara, da suka hada da Bichi, Bagwai, Shanono, Tsanyawa, Kunchi, Makoda, Danbatta, Dawakin Tofa da kuma Tofa.

A yau ne dai ake sa ran gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai rattaba hannu akan wannan doka kana daga bisani ta fara aiki gadan-gadan.

A saurari cikakken rahoto daga wakilin Sashen Hausa, Mahmud Ibrahim Kwari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG