Wani masanin lafiya a Lagos, Dr. 'Kunle Adeyemi-Doro, da yake bada wata kasida yayin wata lacca da Healthway Communication game da hadin gwiwar Sunnu Kuku Foundation domin tunawa da ranar a Lagos, ya lura cewa yin gwaji a kai akai ya zama dole domin cutar ta zamo cuta dake yin kisa a boye.
Adeyemi-Doro wanda ya yiwa kasidarsa lakami da ‘Ciwon suga, yaduwar ciwon da kuma kulawa da mutane masu dauke da ciwon suga,” ya baiyyana ta a matsayin wani abu mai daukar dogon lokaci wanda ake ganinsa ta wurin karuwar suga a cikin cikin jini.
Ya bayana cewa ana samun irin wannan sikarin daga abinci ne, musamman abinci mai sikari sosai, wanda jiki yakan farfasa a ya mayas dashi wani makamashi domin ba jiki karfi. Ya ci gaba da bayyana cewa jikin kuna insulin.
Adeyemi-Doro yayi nuni da cewa insulin na da mahimmanci kwarai, ya da irin wannan sikarin zuwa gabobin jikin dake da bukatarsa. Ya kuma kara da cewa ciwon suga yakan zo ne a lokacin da jikin ya kasa samar da isasshen wannan sinadarin da ake kira insulin wanda yake haifar da sikari ya taru yayi yawa a cikin jinni. Masannin ya bayyana cewa akwai ciwon suga iri dabam dabam inda ya bayyana ciwon suga iri na farko a matsayin yanayin da jiki yakan kasa samar da insulin domin gabobin jikin da suke da alhakin fitar da insulin din sun lalace. Irin wannan yakan sa dole ne mutum ya rika karbar alular insulin. Irin wannan ciwon sugan yawa da yawa a cikin yara.
“Iri na 2,” in ji Adeyemi-Doro “yana shafar manyan ne, kuma yana nunawa ta wajen kasawar jiki ya tanada isasshen insulin ko kuma lokacin da jiki baya iya yin kyakyawan amfani da insulin din da yake samarwa.
Adeyemi-Doro ya kara cewa akwai iri na 3, wanda yake da dangantaka da juna biyu wanda kuma ake yawan samu wajen mata masu ciki yana nanata cewa yawancin lokaci yawan suga a jikin yakan daidaita kansa bayan matar ta haihu.
Yayinda yake Magana kan abubuwan dake iya haifas da ciwon suga iri na 2, malamin ya ambaci shekaru (sama da 40); tarihin iyali; kabila, kiba/nauyi; motsa jiki, hawan jinni da dai sauransu.
Wani mamban dattawa na kungiyar Sunny kuku, Mr. Kunle Ogunade ya baiyyana cewa a shirye kungiyar take tayi yaki da wannan cutar domin kawar da ita, yayinda kungiyar take shirin kafa wuraren shan maganin ciwon suga a kowane yanki na kasar.