Kungiyar tace matsalar rashin tsabta a cikin birnin mai dauke da mutane miliyan biyu, ta sa an shiga dibar ruwansa daga gwurbatattun rijiyoyi da kuma fassassun famfuna.
"A yawancin kauyuka babu ruwan sha ko na wanka, akwai ruwan gwata ko ina akan hanya, akwai gudawa da cutar taifoid da kuma barazanar sake barkewar kwalara,” in ji Tiseke Kasambala, directa na Kare hakin yan adam na kudancin Africa.
Darektan ya kara da cewa "Ruwan sha da yanayin tsabta na Harare sun tabarbare kuma gwamnati bata dauki wani mataki na gyara su ba.”
Rahoton wajen shafi 60 da aka bayas yayi gargadin cewa tarihi ya nuna hatsarin dake tattare da yin ko’oho da al’amarin. Tabarbarewar yanayi a shekara ta 2008 ya haifas da barkewar kwalara wadda ta kashe mutane 4,200 ta kuma kama mutane wajen 100,000.
Ko da yake cutar tana da hatsari kwarai, za’a iya kare ta ta wajen tsabtace ruwa da kuma gwata. Kungiyoyi na agaji sun yi ta tanadas da magunguna da kuma tona rijiyoyi tun daga shekara ta 2008 sai dai rahotanni suna nuna cewa wadansu daga cikin rijiyoyin sun gurbata da ruwan kwatami. Da yawa daga cikin yankunan Harare basu da ruwan pampo kuma ya zamar wa mutane dole su yi layi na awoyi domin su sami ruwa.
"Ruwan sha da yanayin tsabta na Harare sun lalace, sakamakon shekaru na rashin lura da kuma cin hanci da rashawa,” inji Kasambala.