A daya daga cikin kasidun, Seye Abimbola na Hukumar Kiwon Lafiya tun daga tushe ta Najeriya, da wasu marubutan daga kasashen uku sun ce tilas gwamnatoci da hukumomi su dauki matakan samun yardar jama'a, su kuma bayar da muhimmanci ko fifiko ga bayar da rigakafin cutar Polio a lokutan ayyukan rigakafi na yau da kullum da aka saba.
Marubutan suka ce dabarun da ake amfani da su na yaki da cutar a wadannan kasashe uku a yanzu, watakila ba su ne suka dace da yanayin wadannan kasashen ba.
Marubutan suka ce gurin hukumomin kiwon lafiya na duniya na kawar da wannan cuta ta Polio watakila ya rufe musu ido daga irin darussan da aka koya dangane da tsare-tsaren kiwon lafiya na kasashe cikin shekaru 30 da suka shige.
Suka ce, "Za a iya kawar da cutar Polio ce kawai idan aka karfafa tsare-tsaren kiwon lafiya, da kuma sanya hannun jama'a, watau a faro daga kasa, can kasa, maimakon daga sama zuwa kasa. Watakila wannan zai bukaci karin lokaci da karin kudade fiye da wanda aka ware ko ake da su yanzu haka a Najeriya da Pakistan da Afghanistan a saboda yanayin siyasar kasashen,"