Shirinmu na nishadi a yau na mussaman ne, domin kuwa a makon da ya gabata ne masana’atar Kannywood, ta yi babban rashin na mai shiryawa da kuma daukar nauyi a masana’antar, margayi Malam Rabiu Haruna Arrahuz, wanda ya rasu a ranar Asabar da ta gabata.
Don haka ne muka samu damar zantawa da jami’in hulda da jama’a na Kungiyar MOPPAN reshen jihar Kano, malam Murtala Balarabe Baharu wanda ya bamu kadan daga cikin yadda suka gudanar aiki da marigayin da kuma irin rawar da ya taka a masana’antar ta Kannywood.
Mal Rabiu dai an haifeshi ne ranar 1 ga watan Junairun 1978, kuma ya shafe kimanin shekaru 15 yana masana’antar kannywood, mai shiryawa ne kuma mai bada umarni, sannan a hannu guda kuma dan kasuwa ne.
Marigayi dai a ta bakin mal Baharu, mutun ne jajirtacce, mai hakuri sannan mai kwazo wajen kasuwancin fina-finan da yake shiryawa, sannan kuma ya fitar.
Ya ce yakan yi fina-finai dake dauke da labarin da zai tsumma zuciyar mai kallo, sannan mutun ne da baya gajiya a yanayi da aikin shirya fina-finai, mai gaskiya da baya nuna bangaranci kamar yadda malam Baharu ke bayyanawa.
Daga cikin fim din sa akwai fim mai waka ta sakataye, ko masar Bauchi wanda ya fito a cikin wani fim da ya fitar.
Facebook Forum