Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Marasa Rinjaye A Majalisar Dokokin Ghana Sun Kalubalanci Hana Shigar Da Shinkafa Cikin Kasar


Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo

Marasa rinjaye a majalisar dokokin kasar Ghana sun shiga cikin jerin al'ummar kasar da ke bukatar gwamnatin ta janye matakin hana shigar da wasu kayayyaki ciki har da shinkafa da yankakkun kaji da dai sauran kayayyaki da ake shiga da su cikin kasar daga kasashen waje.

A ganin su, matakin zai sa talakawa kara shiga cikin mawuyacin hali a kasar ta Ghana.

Kiran na 'yan majalisar na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin kasar ta sanar da aniyar ta na hana shigar da wasu kayayyaki daga kasashen waje, a kokarin da ta ke yi na neman karfafa darajar kudin kasar wato sidi, da tabbatar da dogaro da kai.

Hon Bawa Muhammad daya ne daga cikin wakilai a bangaren marasa rinjaye a majalisar dokokin Ghana, ya shaidawa muryar Amurka cewa ba sa ra’ayin dokar, kuma har in aka gabatar da ita a gaban majalisar dokokin kasar, ba za su amince da ita ba saboda matsalar tsadar abinci da cin hanci da rashawa da ke karuwa a kasar.

“yau a Ghana kowa ya san cewa nau’ukan abinci da muka fi amfani da su sun hada da shinkafa da yankakkun kaji da man dahuwa da dai sauran su. Dan haka duk wani matakin da gwamnati za ta dauka na hana shigowa da wadannan kayayyaki daga ketare, har in babu wasu tsare tsaren da za su taimaka wa kasar ta sa mu dogaro da kai, to za’a fuskanci karancin wadannan kayayyaki kuma hakan zai haifar da tsadar farashin su. A don haka a bangaren mu na marasa rinjaye a majalisar dokoki bama goyon bayan samar da wannan doka kuma wannan doka har in aka kawo ta zauren majalisa, to shakka babu zamu yi kokari da yawan mu a majalisa mu hana wannan doka motsa wa ko nan da can”

Muhammad Awwal mai shigar da kayan abinci a Ghana, musamman yankakkun kaji da ga ketare, ya bukaci gwamnati ta sake duban wannan matakin saboda hana shigar da wadannan kayayyakin abinci cikin kasa zai shafi kowa ba su kadai ba .

Yace Ghana ba za ta iya yin dogaro da kanta wajen samar da abinci ga al'ummar ta ba, domin haka wannan yunkuri zai janyo damuwa sosai ga 'yan kasa.

Rahotannin baya-bayan nan sun nuna cewa Ghana ta kashe zunzurutun kudi dalar Amurka miliyan 560 wajen shigar da shinkafa daga waje a shekarar 2022 kadai, lamarin da ya zaburar da gwamnati ga tunanin daukar matakin hana shigowa da wasu kayayyakin abinci cikin kasar.

Yusuf Fofana mai magana da yawun gwamnati a fannin bunkasa harkokin zamantakewar jama'a ya ce, Ghana na bukatar wannan doka domin ta ci gaba da dogaro da kan ta.

“wannan dokar ya kamata ta tabbata domin kasar ta samu amfanin arzikin ta. Dalar Amurka da zamu fitar waje mu kawo wadannan kayayyakin duk za su saura cikin kasar. Kowace dala da zaka kai China ka sayo kaya, kamar ka ba matasan China aikin yi ne, a don haka,har idan muka zuba wadannan kudaden a cikin harkokin cikin gida, matasan Ghanaza su samu sana’ar yi. Kuma hakan zai sa kasa ta cigaba”

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG