Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta soma ganawa da masu ruwa da tsaki da suka hada da bangarorin biyu don gano bakin zaren magance wadannan matsaloli.
A wajen taron da rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta shirya, inda aka gayyato bangarorin da abin ya shafa da masu ruwa da tsaki, kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Olugbenga Adenyenju ya ce, dole ne a samo hanyar magance wannan matsala.
DSP Suleiman Yahya Nguroje, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ya bayyana cewa, hakki ne na gwamnati wajen tabbatar da zaman lafiya, kuma rundunar ‘yan sanda a shirye take wajen bada gudunmawar ta don ganin an tabbatar da zaman lafiya.
Daya daga cikin mahalarta taron, Honorabul Hussaini Gambo Bello Nakura ya ce kafin tabarbarewar lamura, manoma da makiyaya tamkar Danjuma ne da Danjummai.
Alh. Muhammad Suleiman Gwalam, shugaban kungiyar manoman auduga a jihar Adamawa ya ce, ya kamata shugabannin wadannan kungiyoyi su dinga tsara al’amuran.
Ga Ibrahim Abdul'aziz da cikakken bayani:
Facebook Forum