Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City za ta fafata gasar Zakarun Turai a kakar wasanni mai zuwa, bayan da a yau Litinin, kotun musamman ta lamurran wasanni ta yanke hukuncin dage haramcin da aka yi wa kungiyar daga shiga gasannin nahiyar Turai na tsawon kakar wasanni biyu.
A watan Fabrairun da ya gabata ne hukumar kwallon kafar Turai wato UEFA, ta yankewa City din wannan hukuncin, bisa laifin sabawa dokokin da suka shafi kudade, wanda nan take kungiyar ta daukaka kara.
An zargi kungiyar da aringizon yawan kudaden shiga daga masu daukar nauyi da ke da alaka da rukunin kamfunan Abu Dhabi, wadanda su ma mallakar mai kungiyar ta city ne Sheikh Mansour, domin kaucewa fadawa dokokin shirin a tsakanin shekarun 2012 da 2016.
Hukumar ta UEFA ta kaddamar da bincike bayan da wata jarida ta wallafa wasu jerin sakwannin email a shekara ta 2018.
Duk da ya ke kotun ta musamman ta sha’anin wasanni ta gano cewa City din ta kasa baiwa jami’an UEFA hadin kai, to amma ta ce kungiyar ba ta saba dokar raba dai-dai na kudaden daukar nauyi ba, inda ta ce kuma akasarin zarge-zargen da aka yi wa kungiyar, ba’a tabbatar da su ba, yayin da wasu kuma sun faru lokaci mai tsawo da ya wuce.
Haka kuma kotun ta rage yawan kudin tarar da aka dorawa kungiyar daga Yuro miliyan 30 zuwa miliyan 10.
Facebook Forum