Ministan Shari'a na Najeriya Abubakar Malami, ya musanta zargin da ake yi masa, na bin hanyar da ke kama da zamba cikin aminci, a kokarin karbo bashin da gwamnatin Najeriya ke bin kamfanonin mai, da ya kai dala biliyan 62.1.
Zargin ko rade-radin, ya biyo bayan daukar kwangilar wani kamfani mai suna Trobel International da ya yi don karbo kudin da ba shi la'adar da ta kai dala biliyan 2.15 wato Naira biliyan 774.
A lokacin da gwamnatin Buhari ta hau mulki a 2015, ta gaji shari'un da suka aza mata biyan Naira biliyan 150 a cewar Malami, wanda ya kara da cewa hakan ne ya sa tantance irin wadannan lamura don gano sahihan ikrari da kuma na cin hanci da rashawa ke da muhimmanci.
Kakakin Ministan Umar Gwandu, a wata sanarwa, ya musanta zargin da ake wa Ministan da cewa ba shi da wata rufa-rufa kan lamarin da ma in an kwatanta da yadda gwamnatin baya wacce kan ba da kashi 30% ko fiye don karbo irin wadannan basuka.
Za a iya tunawa, Malami ya taba ba da amsa kan dalilan da ya sa ya dakatar da ba da la'ada ga wani dan kwarmato Dr.George Uboh kan gano kudin gwamnati sama da Naira biliyan 473 da la'adar ta ta kai Naira biliyan 23.6.
A saurari cikkaken rahoto cikin sauti:
Facebook Forum