Yanzu haka a Najeriya ana ta cece-kuce game da halin kiwon lafiyarsa da ma rayuwarsa baki ‘daya, tun lokacin da ya tafi Ingila hutun shekara-shekara da ya saba.
A wata sanarwa da Femi Adesina, mai baiwa shugaban Najeriya shawara akan harkokin yada labarai, yayi tur da Allah wa dai da wasu ‘yan Najeriya musamman ‘yan adawa dake amfani da wannan ziyara da duba kiwon lafiyar shugaban kasa a matsayin abin cece-kuce, na cewa yana cikin tsananin rashin lafiya ko ma ya rasu.
Yace gwamnati na nan akan bayanin da ta bayar tun farko cewa shugaba Buhari yana hutu ne kuma zai yi amfani da lokacin hutunsa domin likitoci su duba lafiyarsa.
Alhaji Umaru Dembo, ‘daya daga cikin iyayen jam’iyyar APC a Najeriya, ya nuna damuwar kan ra’ayoyin da ke fitowa daga gurin ‘yan Najeriya.
Domin karin bayani saurari rahotan Umar Faruk Musa.