Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makwaftaka Ta Gari Nada Mahimmanci Ga Samun Tsaro a Kasashen Afirka - Buhari


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaba Buhari ya sake nanata mahimmancin hadin kai tsakanin shugabannin kasashen Afirka saboda tabbatar da tsro

Jiya a Abuja Shugaba Muhammad Buhari yace abubuwan dake faruwa kwanan nan sun nuna cewa lokaci yayi da Najeriya da sauran kasashen Afirka zasu manta ba banbance banbancensu su hada kawunansu su yaki ta'adanci.

Yayinda yake jawabi lokacin da ya karbi bakuncin manzo na musamman na shugaba Obiang Nguema Mbasogo shugaban kasar Equatorial Guinea, Shugaba Muhammad Buhari yace tunda ta'adanci bai san iyakokin kasashe ba wajibi ne al'ummomin kasa da kasa su hada kai su kirkiro dabaru cikin gaggawa da zasu inganta tsaro.

Saboda haka makwaftaka ta gari nada mahimmanci wurin inganta tsaro da cigaban tattalin arzikin kasashen Afirka inji Shugaba Buhari.

Shugaban ya cigaba da cewa "Ta'adanci bai san iyakokin kasashe ba. Saboda haka dole ne mu cigaba da inganta matakan yaki da ta'adanci da wasu laifuka na kan iyakoki"

"Irin wannan tunanenda nake dashi ya sa na ziyarci duka kasashen dake makwaftaka da Najeriya cikin 'yan kwanaki kadan da na karbi shugabanci kuma zamu cigaba da iyakar kokarinmu mu karfafa dangantaka a yankinmu da ma kasashen duniya domin yaki da ta'adanci" inji Shugaba Buhari.

Manzon na musamman Mr. Agapito Mba Mokuy ya fada ma Shugaba Buhari cewa tsaron Najeriya yana da mahimmanci ga duka kasashen yammacin Afirka.

Mr. Mokuy wanda kuma shi ne ministan harkokin waje da hadin kai na kasar Equatotorial Guinea yace Shugaba Mbasogo ya yaba da cigaban da Najeriya take samu a karkashin shugabancin Muhammad Buhari na kawo karshen tashin tashinar Boko Haram.

Daga bisani ya mika wasikar gayyata daga Shugaba Mbasogo wa Shugaba Buhari ya kai ziyara Equatorial Guinea a duk lokacin da ya dace masa.

XS
SM
MD
LG