Ganin cewa ya kamata ta dan kara wa'adin dokar ta baci a yankin Diffa ya sa gwamnatin kasar ta Nijar ta nemi amincewar majalisar dokokin kasar da yin hakan.
Yanzu dai gwamnatin ta nemi tsawaita dokar na karin tsawon watanni ukku kafin a ga abun da hali yayi kamar yadda ministan tsaron kasar Mukhtari ya sanarwa majalisar.
Bayan yin nazari a kan bukatar gwamnatin duka 'yan majalisar ne suka amince da karin wa'adin dokar ta bacin na tsawon watanni ukku. 'Yan majalisan suka ce magana ce da ta shafi soja saboda haka nasu dai su goya masu baya tare da yin addu'a Allah ya ba kasar Nijar zaman lafiya.
To saidai dan majalisa daga bangaren Diffa Lamido Mummuni Haruna yace kafa dokar ta baci yana da faida idan aka fitar da tsaro. Yace daukan irin wannan matakin na tsawaita dokar ta baci yakamata gwamnati ta dauki hanyoyin inganta rayuwar jama'a musamman hanyoyin fadada harkokin arzikin mutanen da abun ya shafa. Yakamata a samar ma matasa ayyukan yi domin kaucewa fadawa tarkon Boko Haram.
Inji Onarebul Lamido Mummuni Haruna kungiyar Boko Haram na neman sabbin mayaka ta kowane hali kuma yakamata mahukunta su lura da hakan. Yace a can baya mutanen yankin na Diffa sun koka da yadda dokar ta bacin ta shafi noman tattasai. Noman tattasai shi ne hanyar da mutanen yankin ke samun kudaden shiga domin suna anfana da ruwan kogin tafkin Chadi da na kogin Komadugu.
Talakawan na zargin jami'an tsaro da wuce makadi da rawa a ayyukan tsaro da su keyi.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.