Sun amince ne ko bayan da aka jefa kuri’a, yayin da kuriu 397 suka rinjayi kuriu 223.
Firayim Minista David Cameroon ya bayyana gaban majilisar domin ya kare wannan bukatar, yana cewa kai hari ta sama zaifi muhimmaci kwarai da gaske fiye da wanda suke kaiwa ta kasa yace ta haka ne za a iya kakkabe kungiyar ta ISIS.
Dama dai Birtaniya ta share sama da shekara guda tana kai hari a Iraq, Cameroon ya nemi ne da a kara wa’adin aikin amma wannan karon har zuwa Syria inda nan ne tungan yan ISIS ta yammaci.
Sai dai kafin wannan bukata ta samu amincewa sai da aka kwashe saoi goma ana tafka muhawara kafin a cimma matsaya.
Shugaban yan Adawa na jamiyyar Labour Jeremy Corbyn ya soki wannan bukata da kakkausan lafazi yace Firayim Minista Cameroon ya kasa kafa kwakkwaran hujjan da zai gamsar da mutane dalilin da zaisa Birtaniya daukar wannan matakin.