Wakiliyar hukumar Majalisar Dinkin Duniya Alexandra Morelli, mai kula da 'yan gudun hijira a jamhuriyar Nijar ta ziyarci garin Agadez, inda ta gana da hukumomin jihar, da babban alkalin jihar.
Wannan ziyarar na zuwa ne bayan da hukumomin shari'a suka tsare wasu 'yan gudun hijira su 335 a garin Agadez kamar yadda babban alkali mai shigar da kara na Agadez ya bayyana.
Alexandra Morelli ta fadi cewa ta je Agadez ne domin ta nuna goyon bayanta ga hukumomin wannan jihar, da kuma duba wannan matsalar don gano yadda za a warware ta.
Morelli ta kara da cewa hukumarsu zata yi kokarin gano hanyoyin da suka dace a bi don kaiwa wasu daga cikin 'yan Sudan da wannan matsalar ta rutsa da su agaji.
Malam Sadu Saloke, gwamnan jihar Agadez, ya godewa tawagar ta hukukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalaisar Dinkin Duniya, kana ya kuma bayyanawa wakiliyar yadda Nijar take dawainiya da 'yan gudun hijira, wadanda daga bisani suka fara nuna halaye marasa kyau.
Saloke ya ce 'yan gudun hijirar basa sauraren su, kuma suna karya dokoki da lalata kayan gwamnati da kuma na jama'a, bayan haka sun bar yara a waje cikin sanyi, abinda ya sa dole aka dauki matakin da ya kai ga hukumomi tsare 'yan gudun hijira 335 da ake bincike akan su domin gano wadanda ke da laifi a cikin su.
Shugabar reshen 'yan gudun hijira ta Nijar, ta ce a matsayin ta na mace, kuma uwa ta ji zafin abinda ya faru musamman game da yaran. Sannan ta bukaci hukumomin Nijar su samarwa yaran kariya da yanayin kwanciyar hankali.
A saurari cikakken rahoto cikin sauti daga Agadez.
Facebook Forum