Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Brazil ta dakatar da shugabar kasar Dilma Rousseff


Dilma Rousseff bayan majalisar dattawan kasar ta dakatar da ita daga kan mulki.
Dilma Rousseff bayan majalisar dattawan kasar ta dakatar da ita daga kan mulki.

'Yan majalisar dattawa 55 suka amince da dakatar da shugabar kasar yayin da 22 suka ki, lamarin ka iya kaiga tsigeta gaba daya nan da watanni shida bayan binciken da za'a yi akan zargin yin magudi a kasafin kudin kasar.

Shugabar Brazil Dilma Rousseff da majalisar dattawan kasar ta dakatar daga mulki ta sha alwashin cigaba da yaki da matakin majalisar.

Yanzu dai an cireta daga mulkin kasar na dan wani lokaci saboda zargin yin magudi da rufa-rufa da kasafin kudin kasar da ake yi mata kuma tuni aka rantsar da mataimakinta Michel Temer wanda ya maye gurbinta.

Yayinda ministocinta suke kewaye da ita suna hawaye, Rousseff a jawabinta na karshe daga fadar gwamnati ta haikance bata aikata wani laifi ba ta kuma nanata abun da ta saba fada cewa dakatar da ita tamkar juyin mulki ne.

Tace abun da ya fito karara shi ne rashin mutunta zabe da amincewa da muradun jama'ar kasar Brazil da suka zabi shugaban kasa da kuri'unsu. Tace abun takaici ne yadda aka karya kundun tsarin mulkin kasar. "Ko da mafarki ban taba tsamanin zan sake yaki da juyin mulki ba" inji Rousseff. Dama can tsohuwar 'yar yakin sunkuru ce yayin mulkin kama karya na sojoji kusan shekaru arba'in da suka gabata

Shugabar 'yar shekaru 68 da haihuwa mai ra'ayin 'yan gurguzu ta daga wa masu goyon bayanta hannun bankwana na wani dan lokaci kafin ta koma cikin fadar shugaban kasa inda zata cigaba da zama yayinda ake cigaba da shari'arta.

Tsohon abokin aikinta kuma mataimakinta da ya juya mata baya Michel Temer mai ra'ayin mazan jiya tuni ya kafa gwamnatinsa tare da nada ministocin da yawancinsu 'yan jari hujja ne. Ministocin ne zasu lalubo hanyoyin farfado da tattalin arzikin kasar da yanzu ya komade tatas. Zasu kuma duba yadda zasu sake tsara maganar fansho.

Michel Temer yace yanzu ba lokacin biki ba ne ko baza koli, lokaci ne na tunani da yin takatsantsan saboda irin halin tabarbarewa tattalin arziki da kasar ke ciki. Dole mu tashi mu gyara harkokin kasuwanci da cinikayya, mu gyarawa 'yan kasuwa masu zaman kansu yanayin kasuwanci kana mu sake gyara kasafin kudin kasar" inji Temer.

Michel Temer, sabon shugaban Brazil natsawon watanni shida lokacin da ake shari'ar shugabar kasar da yanzu aka dakatar da ita
Michel Temer, sabon shugaban Brazil natsawon watanni shida lokacin da ake shari'ar shugabar kasar da yanzu aka dakatar da ita

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG