Kafafen yada labaran kasar Brazil sun bada rahoton cewa wani babban lauyan gwamnatin kasar ya na neman kotun kolin kasar ta fara gudanar da bincike akan zargin hana wa ma'aikatun shara'a gudanarda aiyukkansu da tsohuwar shugaba ,Dilma Rousseff ta yi.
Jami’ai dai basu tabbatar da sahihancin wannan rahoton ba, wanda ya fito a yammacin jiya Talata. kamfanin dillacin labaran Blobo News na Brazil, ya fadi cewa, ana zargin Rousseff da kokarin hana bincike akan wani kamfanin mai mallakar gwamnatin kasar, mai suna Petrobras.
Jaridun kasar Brazil sun ambaci alkali Rodrigo Janot yana cewa, ya nemi izini akan a gudanar da bincike kan Rousseff da kuma shugaban da ta karbi mulki a hannunsa, abokinta kuma, Luiz Inacio Lula da Silva. An fadi cewa binciken da za a gudanar za a yi shi ne wayar tarho tsakanin su biyun.
Dama ana binciken Rousseff akan wani batu na dabam kuma ta yiwu ta fuskanci batun tumbukewa nan da mako mai zuwa. An zargi Rousseff da laifin boye wasu kudade a kasafin kudin shekarar 2014 na kasar don shirin sake tsayawa takara. Amma Rousseff ta karyata duk wadannan zarge-zargen.
Rousseff ta ce fara shirin tumbuke ta daga mukaminta zai iya dagula siyasar kasar.