Majalisar Dattawan Amurka ta amince da fitar da kudin shirin bada agaji na dala Tiriliyan 2 da zummar taimaka wa jama’a da sana’o’i don su iya jure mawuyacin yanayin tattalin arziki da kalubalen kiwon lafiya da ake fuskanta a kasar yanzu sakamakon annobar cutar coronavirus.
A jiya Laraba ne majalisar ta amince da kudurin dokar, wanda ya sami goyon bayan dukkan ‘yan majalisar daga jam’iyyu 2. Yanzu haka kudurin dokar ya isa gaban zauren majalisar wakilai, inda ake sa ran shugabannin majalisar zasu kada kuri’a akansa ranar Juma’a 27 ga watan nan na Maris.
Shugaban Amurka Donald Trump ya fada wa manema labarai a fadarsa ta White House a jiya Laraba cewa, zai gaggauta aiwatar da dokar bayan amincewar majalisar dokoki. Ya kuma ce ranar da za’a rattaba wa dokar hannu, za ta kasance muhimmiyar rana ga ma’aikatan Amurka, da iyalai da kuma kamfanonin Amurka.
Facebook Forum