Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bakari A Matsayin Jagorar Hukumar NFIU


Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)
Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)

Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da nadin Hafsat Bakari a matsayin darakta a hukumar kula da hada-hadar kudi ta Najeriya wato NFIU.

Tabbatar da Malama Hafsat a matsayin darakta ya biyo bayan nazarin rahoton kwamitin yaki da cin hanci da rashawa dake samun jagorancin Sanata Emmanuel Udende Memga da ke wakiltar mazabar Binuwai ta arewa maso gabas a majalisar.

A makon jiya ne shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Hafsat Bakari a matsayin Darakta kuma jagorar hukumar ta NFIU tare da mikawa ga Majalisar Dattawa don tabbatar da ita.

A yayin fitar da sanarwa a kan nadin Hafsat, mai magana da yawun Shugaban Tinubu, Cif Ajuri Ngelale yace Malama Bakari lauya ce kuma kwararriya a fannin binciken harkokin kudi, wacce ta shafe shekaru da dama a fannin yaki da safarar kudaden haram, daukan nauyin ta’addanci, da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

A cewar Ngelale, kafin a nadin Shugabar Hukumar ta NFIU, ta taba zama mataimakiyar darakta a sashin kula da harkokin kudi na hukumar, kuma ta kasance Shugabar sashen kula da harkokin yau da kullum a lokuta daban-daban, baya ga shugabantar sashen tsare-tsaren dabaru da jagorantar sakatariyar kwamitin hukumar ta hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Bayan nadin ta, Shugaban Kasa na sa ran cewa, Hafsat Bakari za ta yi amfani da kwarewa da gogewarta wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta a wannan muhimmin aiki da aka bata, musamman ganin yadda gwamnatin Shugaba Tinubu ke kokarin yaki da masu safarar kudade ta haramtacciyar hanya, da sauran ayyuka aikata almundahana da kudadden al’umma da a halin yanzu ake gani a bangaren kasuwannin canjin kudadden waje na kasar nan, in ji Ngelale.

Tun bayan fitar da sanarwar Malama Hafsat ne wasu ‘yan Najeriya ke ta tafka muhawara a kan cewa Allah ya sa kar ta baiwa mutane kunya kamar wasu mata da aka baiwa mukamin musamman na baya-bayan nan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG