Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Bayanin Canji A Tsarin Tantance Ministoci A Majalisar Dattawan Najeriya


Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki

Yayin da jama'a ke ta korafe-korafe game da batun sabbin Ministocin da za a nada a Najeriya, an yi bayanin sauyin da aka yi wajen tantance wadanda za a nada din da kuma kokarin da ake yi na ganin an tantance tsohon gwamnan jahar Rivers cikin natsuwa.

Wani dan Majalisar Dattawan Najeriya ya yi bayanin dalilin da ya sa aka canja tsarin tantance Ministoci a Majalisar Dattawan Najeriya ta yadda a maimakon goma a yanzu ake tantance uku kawai a rana. Da ya ke bayani ma wakiliyar Sashin Hausa Madina Dauda, Sanata Ali Ndume ya ce abin da ya sa aka canja tsarin shi ne mutane sun yi korafin cewa tantance Ministoci goma a rana ya yi yawa. Y ace su kansu ‘yan Majalisar wasunsu na korafin cewa bas u samun damar yin tambayoyi ga wadanda ake tantancewar saboda sun yi yawa.

Sanata Ndume y ace saboda korafin na jama’a da ‘yan Majalisar Dattawan sai aka yanke shawarar cewa dayake saura mutane goma sha takwas a tantance, za su dau mutane uku-uku cikin gwanaki shida da ake zama za a dau sati biyu a kammala tantancewar. Ya ce wannan zai ba su damar duban sauran ayyukan Majalisar tunda ba aikinsu shi ne tantance Ministoci kawai ba. Ya ce akwai wasu kudurorin da aka gabatar da ke bukatar dubawa baya ga batun tantance Ministocin.

Game da batun kurar da ta taso game da batun tantance tsohon gwamnan Rivers Rotimi Amaechi, Santa Ndume y ace sun a kan ba da hakuri shi ma ya na tattaunawa da su dayake batu ne na siyasa. Ya ce za su gabatar da shi koma kuma da yaddar Allah ba za su sami wata matsalaba. Ya ce sabanin kama karyar da y ace an yi a gwamnatin PDP a yanzu so su ke su bi tsarin da ya dace da doka. Amma ya ce idan kura ta kai bango, to za su nuna ma ‘yan adawa cewa su ke da rinjaye.

Ga Madina Dauda da cikakken labarin:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG