Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Gudanar Da Taron Kasa Kan Yaran Da Basa Zuwa Makaranta   

Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)
Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)

A zazzafar mahawarar da fiye da sanatoci 20 suka tafka, an bayyana matsalar yaran da basa zuwa makaranta da wani bam dake daf da fashewa, dake bukatar daukar matakan da suka zarta na gwamnatin tarayya kawai.

A kokarinta na shawo kan matsalar yaran da basa zuwa makaranta, Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci a gudanar da taron kasa bayan data gana da Shugaba Bola Tinubu.

An yanke wannan shawara ne yayin zaman majalisar bayan da kwamitinta a kan ilimin firamare da sakandare ya gabatar da rahoto a kan matukar bukatar shawo kan matsalar yaran da basa zuwa makaranta a Najeriya.

Shugaban kwamitin, Sanata Usman Lawal Adamu, mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya bayyana cewar a cikin shekara daya an yi nasarar shigar da fiye da yara miliyan 2 makaranta ta hanyar kokarin hukumomin ma’aikatar ilimi dake aiki a kan yaran da basa zuwa makaranta.

A zazzafar mahawarar da fiye da sanatoci 20 suka tafka, an bayyana matsalar yaran da basa zuwa makaranta da wani bam dake daf da fashewa, dake bukatar daukar matakan da suka zarta na gwamnatin tarayya kawai.

A cewar Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, yaran da basa zuwa makaranta ‘yan bindiga ne da ake reno, abin da ya kara jaddada bukatar magance matsalar.

Gaba dayan majalisar ta amince da kudirin gudanar da taron kasa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG