Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisa Ta Yi Wa Dokar Hukumar Kula Da Zuba Jari Ta Kasa Kwaskwarima


Sanata Mohammed Tahi Mungono
Sanata Mohammed Tahi Mungono

Majalisar Dattawan Najeriya ta yi kwaskwarima ga dokar hukumar kula da Zuba Jari ta kasa wacce aka fi sani da NSIP, da nufin dauke hukumar daga ma'aikatar agaji da rage talauci zuwa fadar shugaban kasa. Amma kwararre a fannin zamantakewar bil'adama na ganin abin ba zai canja zani ba.

Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa Opeyemi Bamidele, shi ne ya kawo kudurin gyaran dokar, inda ya bayyana cewa manufar tsarin na da kyau, sai dai ba a ba da dama tsarin ya cimma manufofin kafa shi ba.

Opeyemi ya ce a majalisa ta 9 aka amince da kudurin amma an gano cewa aiwatar da shi na da kura-kurai, domin wadanda ya kamata a basu goyon baya wajen cin moriyar tsarin a yankunan karkara ba su ne suka amfana ba.

Sanata Mohammed Ali Ndume yana cikin masu irin wannan tunanin, inda ya ce wadanda aka ba su damar aiwatar da tsarin sun yi babakere a kai, ba su ba da dama majalisa ta sa ido a kan yadda aka gudanar da tsarin ba.

Ndume ya ce Majalisa ta amince da dokar da za ta mayar da tsarin zuwa fadar Shugaban kasa ba tare da bata lokaci ba. Ya kara da cewa a yanzu haka Gwamnati tana bincike kan tsarin saboda kar a sake maimaita abin da ya faru a baya.

To ko menene Majalisar za ta yi na daban domin ci gaban shirin duk da cewa bangaren Gwamnati ya dakatar da shirin a yanzu?

Sanata Mohammed Tahir Munguno, ya ce mayar da tsarin a karkashin Shugaban kasa zai fi muhimmanci. Munguno ya ce Shugaban kasa shi ne uwa shi ne uba, babu yadda za a yi a bar mutane su bata tsarin. Ya kuma ce an riga an kashe makudan kudade sai dai ba a bi tsari wajen yin aikin ba, shi ya sa Majalisa ta ga ya dace a mayar da aikin zuwa Fada wajen shugaban kasa, inda aka bashi shawarar ya mayar da tsarin zuwa gundumomi inda za a samu sunayen mutane, a bude masu asusun ajiya ta inda za a aika masu kudaden tallafi, saboda a samu bayanai a lokacin da ake so.

Sanatan ya kara da cewa bai yiwuwa a bar shirin kara zube, babu adireshin masu karbar tallafin.

Amma kwararre a fannin zamantakewar bil'adama kuma malami a Jami'ar Abuja, Dakta Abu Hamisu, ya yi tsokaci yana cewa duk inda aka kai wannan aikin 'yan Najeriya ne za su yi shi.

Abu ya ce ko da an mayar da shi fadar Shugaban kasa za a samu son zuciya a aikin. Ya kara da cewa kamata yayi a bi diddigin wadanda suka yi kuskure wajen aiwatar da aikin a hukunta su, domin ta haka ake samun ci gaba a irin wannan yanayi.

Abu ya ce duk kasashen da suka ci gaba sai sun bi tsari sosai sannan ake samun nasara, kuma a bar tsarin a yadda ya ke da shi ya fi kyau.

A wannan tsari na NSIP akwai batun N-Power wanda shi ne daya daga cikin shirye-shiryen zuba jari wanda Gwamnatin tsohon shugaban kasa Mohammadu Buhari ta kafa domin magance rashin aikin yi a kasar.

Saurari rahoton Medina Dauda:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG