Majalisar tayi zargin yin aringizo wajen tantance matasa da aka bullo da tsarin dominsu.
Wannan shirin dai ya haifar da rikici a kwanakin baya tsakanin Ministan Ma'aikatar Kwadago da ‘yan Majalisar Dattawa har suma su ka dakatar da shirin na wucin gadi.
A yanzu kuma, ‘yan Majalisar Wakilai sun ce sun gano wata manakisa da ake shirin yi a tsarin kamar yadda shugaban Kwamitin Kula da Kaidoji da tsare-tsaren Majalisar, Abubakar Hassan Fulata ya bayana cewa ba a bi kaida wajen tantance sunayen matasa da za a dauka ba.
Fulata ya kara da cewa a binciken da suka yi, sun gano cewa matasan wani bangare na kasar ne kadai za su amfana da tsarin a maimakon na kasa baki daya, kuma yana gani barin shi a haka ba daidai ba ne, dole ne su yi wa tufkar hanci domin su ne wakilan jama'a.
Shi ma Dan-majalisa Mai Kula da Kwamitin Tabbatar da Daidaito Daukan Ma'aikata a Kasa, Abubakar Yahaya Kusada, ya ce duk da cewa bangaren gwamnati ne ke da alhakin gudanar da tsarin, majalisa ce ke amince da bada kudaden da za a yi amfani da su.
Kuma hakin ta ne ta sa ido akan yadda za a tafiyar da tsarin domin kowa ya ci gajiyar shirin.
Majalisar ta bukaci Ma'aikatar Kudi da ta dakatar da sakin kudade da ya kamata ayi amfani da su a shirin har sai an kammala bincike a kan wasu matsaloli da suka taso na ingancin wannan tsarin.
Sannan kuma sun bukaci gwamnati ta hanzarta mayar da Shugaban Hukumar Daukan Ma'aikata ta NDE, Dr. Nasiru Ladan Argungu, a bakin aikinsa.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda: