Daruruwan ma'aikatan ne suka yi cincirindo a zauren majalisar dokokin jihar domin nuna rashin jin dadinsu akan sabon tsarin cire kudaden fansho da ake anfani dashi a jihar.
Tun a shekarar 2007 ne ake anfani da sabon tsarin fanshon da ake cire kashi biyar da digo bakwai daga cikin albashinsu. To saidai sun ce kawo yanzu babu wani wanda ya anfana da shirin.
Tun farko majalisar dokokin jihar ce ta gayyaci ma'aikatan saboda jin ta bakinsu akan sabon tsarin sakamakon korafe-korafe da majalisar tace ta samu.
Kakakin majalisar Ahmed Marafa Guni yace sun yi zaman jin ra'ayin jama'a sabili da koke-koken da suka samu daga ma'aikata da ma jama'ar jihar gaba daya.
Shugaban kungiyar kwadagon jihar Idris Ndaku ya tabbatar da jawabi a gaban majalisar inda yace dole ne a dakatar da cire kudaden. Bayan an dakatar da dokar dole ne kuma a samarda dokar da zata sa a mayarwa kowane ma'aikaci kudinsa.
Wasu ma'aikatan da suka halarci zauren majalisar da suka yi ritaya sun ce sun ajiye aiki amma babu fansho balantana kudin sallama da ake kira gratuity. Wasu ma cewa suka yi kudaden da ake cirewa daga albashinsu basu san inda suke ba.
Bayanai sun nuna cewa akwai miliyoyin nerori a ma'aikatar fansho da ake neman bahasi akansu a karkashin shirin. 'Yansandan fararen kaya ko SSS sun soma gayyatar ma'aikatan fanshon domin bayani.
Ita ma majalisar dokokin jihar ta lashi takobin zakulo gaskiyar lamarin domin tabbatar d adalci.
Ga karin bayani.