Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magu Na Nadawa EFCC In ji Shugaba Buhari


Wasika daga fadar shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, da ta bukaci majalisar dattawan ta sake duba wake mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci, EFCC, Ibrahim Magu, domin zama cikakken shugaban hukumar, ya kawo karshen harsashen wasu sunaye da ake ganin zasu maye gurbin Magun.

Majalisar dai a karshen shekarar da ta gabata kafin tafiya hutu ta sanar da kin amincewa da wanke Magun, rahoto daga hukumar tsaro na farin kaya na DSS, da yace Magu, yayi zarmiya ta hanyar kama masa hayar gida kan miliyan ashirin duk shekara da kudi cin hanci.

Wannan lamarin dai ya kawo takaddama inda har majalisar ta sake maidawa fadar shugaban kasa takardar neman a sake turo sunan wani da za a wanke domin hawa kan wannan kujera mai mahimmaci.

Shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki, ya gabatar da wasikar da shugaba Muhammadu Buhari,ke son wanzuwar aikin EFCC, tun fara aikin Gwamnatin sa ranar 29, ga watan Mayu 2015.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00

XS
SM
MD
LG