Shirin Mata da Sana'a a wannan mako ya sami bakuncin malama Sa’adatu Umar, mace mai kamar maza, wacce ta ce tana sayar da kayan maza duba da yadda mafi akasarin maza ke da kunya da son girma wajen gaggauta biyan bashi. Da zarar sun karbi bashin kaya a wajen mace, sabanin yadda mata suke wajen kararban bashi.
Tun da farko malama Sa’adatu ta ce, ta fara sana’ar sayar da kayan mata ne inda yawaitar karbar bashi ya karya mata jari. Sai da ta fara tara kudin sana’ar tun daga tushe. Daga nan ne ta lura da cewar idan tana son jarinta ya tsaya, sai dai ta daina harka da mata ta koma ga maza.
Sa’adatu ta ce, ta shafe shekaru da dama ta na sana’ar hajja kuma ta fara ne tun ta na aikin gwamnati sai ta zuba kayan sayarwarta a bayan mota wanda a mafi yawan lokuta ta ke aiki kuma ta na sayar wa abokan aikinta tare da baiwa kowanne wato aikin da ta ke yi da sana’ar ta lokacisa.
Ta ce ta na amfani da shafukan sadarwa na zamani kamar su Instagram wajen tallata kayayyakinta ga masu bukata da zarar sun yi mata Magana sai su tsaya yadda za’a aikia wa mutum, duk inda yake a fadin duniya.
Har ila yau ta kara da cewa ta na sayar da takalmin hannu wanda ake yi a nan gida , duba da irin kishin da take yi wa kasar ta kamar yadda ta ke cewa.
Ta ja hankali matasa da su nemi sana’ar hannu komai kankantarsa ko da kuwa da su na wasu ayyukan ko na gwamnati ko akasin haka, sannan ta bukaci ce da su mai da hankali ga dukkanin abin da zasu aika na samun kudaden shiga amma babban abu mafi mahimmanci shi ne su sanya tsoron Allah a harkar neman su.
Facebook Forum