Kwana guda bayan dage babban Zaben Najeriya, masu shari da manazarta, na ci gaba da bayyana ra’ayoyi masu karo da juna dangane da matakin da hukumar zabe ta INEC ta dauka.
A daren ranar Juma’a shugaban Hukumar zaben ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyanawa ‘yan Najeriya cewa, hukumar ta dage zaben, saboda wasu matsaloli da ta fuskanta da suka shafi raba kayayyakin zabe.
Wannan mataki ya sa ‘yan Najeriya na ta yin suka yayin da wasu ke cewa hakan shi ya fiyewa kasar.
“Zai zamanto cewa kasashen duniya za su daina ganin mu da kima, mun kawo jama’a da yawa daga kasashe da yawa, ka ga wannan babbar asara ce domin za ka biya wadanna mutanan ne ko su koma gida.” Inji shugaban Cibiyra Raya Dimokradiyya da Ci Gaba, Dr. Kole Shettima.
A ranar 16 ga watan nan na Fabrairu aka tsara za a yi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu, sannan a yi na gwamnoni a ranar 2 ga watan Maris.
Amma yanzu INEC ta dage zaben na shugaban kasa zuwa 23 ga watan nan, sannan na gwamnoni ranar 9 ga watan Maris.
To amma wasu masu sharhi sun yi maraba da wannan matakin na INEC.
“A jawabin da shugaban INEC Prof. Mahmood ya yi, ya kawo dalilai da yawa, ya ce dagawan da aka yi ya fi alheri akan a ci gaba, domin ya ce idan an ci gaba a haka, za a samu matsaloli.” Inji Dan Masanin Fika, Alhaji Baba Ba'abba mai sharhi kan al’amuran yau da kullum.
Yanzu dai an zuba ido a ga zuwa ranar ta 23, lokacin da za a gudanar da wannan zaben.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina: