Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsar Da Sabon Sakataren Harkokin Wajen Amurka


Sabon Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson
Sabon Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson

An rantsa da Rex Tillerson a daren jiya Laraba a matsayin sabon Sakataren Harkokin Wajen Amurka, 'yan sa'o'i bayan amincewa da shi da Majalisar Dattawan Amurka ta yi.

Mataimakin Shugaban Kasa Mike Pence ne ya rantsar da Tillerson a ofishin shugaban kasa na 'Oval Ofice' da ke Fadar White House a gaban Shugaba Donald Trump.

Tillerson ya gode ma Trump saboda ba shi abin da ya kira 'wata babbar dama' sannan ya ce shi har kullum zai kare muradun Amurkawa ne.

Trump ya jijinawa Tillerson, ya na mai cewa sabon Sakataren Harkokin Wajen mutum ne da ake mutuntawa a fadin duniya don haka zai azruta harkar diflomasiyyar duniya da kwarewarsa da kuma hangen nesansa.

'Yan Majalisar Dattawa na jam'iyyar Democrat uku ne kawai da kuma wani dan majalisa mai zaman kansa su ka bi sahun gamayyar 'yan Republican wajen goyon bayan Tillerson, wanda aka tantance shi da kuri'u 56 akasin 43.

Sanatoci daga duka jam'iyyun biyu sun kashe tsawon makwanni su na tunani kan dangantakar tsohon Shugaban na Exxon Mobil da Shugaban Rasha Vladimir Putin da kuma yadda zai iya fifita aikin diflomasiyya kan kasuwanci.

XS
SM
MD
LG