Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Jinyar Kasar Zimbabwe Na Barazanar Kai Gwamnati Kotu


Ma'aikatan kiwon lafiya a Zimbabwe dake zanga zanga
Ma'aikatan kiwon lafiya a Zimbabwe dake zanga zanga

Ma'aikatan jinya a kasar Zimbabwe na barazanar gurfanar da gwamnatin kasar kotu idan basu biya masu bukatunsu ba tare da janye korarsu daga aiki da gwamnatin kasar ta ce ta yi

Kungiyar nan dake wakiltan ma’aikatar jinya da ungwazomanci sama da dubu 15 a kasar Zimbabwe sun lashi takobin daukar matakin kai gwamnati kotu sai ko idan ta sake shawara na korar ma’aikatan jinya dake yajin aiki a asibitoci mallakar gwamnati.

An tilasta mu ne mun dunfari kotu domin ta kawo muna dauki inji sakataren ma’aikatan na jinya da ungwazomanci Enoch Dongo ya fadi haka ne ko a jiya Alhamis.

A ranar Littinin din wannan satin ne dai ma’aikatan na jinya suka tafi yajin aiki inda suke neman karin albashi, samar da kayayyakin aiki nagari, tare da samar wa kiwon lafiyar kasar kaso mai tsoka a cikin kasafin kudin kasar.

Mataimakin shugaban kasar na Zimbabwe ne dai Constantino Chiwenga ya bayyana cewa muddin ma’aikatan basu koma bakin aiki ba to ba shakka za’a maye gurbin su da wasu domin agaza wa majinyata da kuma ceton rayukan al’umma.

Sai dai har zuwa jiya Alhamis shugaban ma’aiktan kiwon lafiyar Dongo yace kawo yanzu ba wanda ya basu takarda sallama bakin aiki, don haka yanzu su ma’aikatan gwamnati ne.

Amma a wuri ko ministan kiwon lafiyar kasar Dr David Parirenyatwa ya shaidawa kafar yada labarai na kasar ta Zimbabwe cewa ma’aikatan da aka kora idan suna son aikin su to sai sun sake rubuta wata sabuwartakardan neman aiki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG