Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsar da Sabon Shugaban Kasar Zimbabwe


Emmerson Mnangagwa Sabon Shugaban Zimbabwe
Emmerson Mnangagwa Sabon Shugaban Zimbabwe

Sabon shugaban kasar Zimbabwe da aka rantsar da shi a yau Juma’a ya fara jawabin sa na kama aiki da yabawa tsohon kasar Robert Mugabe kuma ya yi alkawarin gudanar na zabe sahihi bisa tafarkin demokuradiyya shekara mai zuwa, kamar yanda aka shirya za'a yi.

Yace yan Zimbabwe su manta da abubuwa da suka faru a baya.

An rantsar da Emmerson Mnangagwa a matsayin shugaban kasar Zimbabwe ne a yau Juma’a a wand a ya kawo karshen mulkin kama-kariya na tsawon sheakru 37 karkashin Robert Mugabe.

Mnangagwa ya kira Mugabe da a 'zaman uban kasar su", yayin da ya kuma ce tsohon shugaban ya tabka kurakurai na kin yin abunda ya dace, da kuma aikata kishiyarta.

Sabon shugaban ya fadawa taron jama’a da suka cike filin wasan na kasa mai daukar mutane dubu 60 a birnin Harare cewar babban aiki dake gabansu shine sake gina kasarsu.

Mnangagwa ya yi alkawarin biyan diyya ga manoma da suka yi hasarar filayen gonakinsu karkashin mulkin Mugabe. Masu sukar lamirin Mugabe sun ce shirin sabonta harkokin filaye, wanda ya tilastawa fararen fata yan kasuwa suka bar gonakinsu, shine ya haddasa yunwa a cikin kasar wanda a wani lokaci ake ganinta mai iya wadata abinci ga shiyyar kudnacin Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG