Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana'izar Dalibin Da Ya Rasu A Zanga Zanga


 Wadanda suka halarci janaizar Mala Bagale
Wadanda suka halarci janaizar Mala Bagale

A jamhuriyar Nijar anyi jana’izar dalibin da ya rasu a zanga zangar da aka yi a makon jiya a birnin Yamai yayinda kungiyar dalibai ke ci gaba da tursasa hukumomin kasar dasu gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata wannan aika aika, koda yake a jiya an tashi baran baran a taron sulhu da ya hada bagarorin biyu.

Dubban dalibai da mazauna birnin Yamai wasu a kafa wasu akan ababen hawasuka yiwa marigayi Mala Bagale, rakiya zuwa makwancinsa na karshe bayan da aka dauko gawarsa daga babban asibiti zuwa makabartar Yantala, duk wanda ka gani cikin wadanda suka halarci jana’izar akan gane bacin rai a fili a fuskokinsu.

Sakatare janar, na kungiyar daliban Nijar Hussaini Sambo, yace gobe idan Allah ya kaimu zasu kai takarda na bukatar neman izinin yin jarin gwano a ‘yan kwanaki masu zuwa domin neman shugaban kasa da ya gaiwa iyayen wanda ya rasu ta’aziya.

Jin takaicin abinda ya sami wannan dalibi a yayinda jami’an tsaro suka kai samame Jami’ar Abdulmumuni a makon jiya da suna murkushe tarzoma yasa shugabanin dalibai ficewa daga zauren taron sulhu da wakilan gwamnati karkashen shugabancin Birji Rafini, da kuma wakilai daga shuwagabanin addinai, da na hukumar kare hakkin bil Adam.

Firaministan Nijar Birji Rafini, yace ficewar shuwagabanin daliban daga zauren taron bai kamata ba yana mai cewa komai sai anyi hakuri da kuma tasa tsantsan.

Hukumar ‘yan Sanda ta bada sanarwar dakatar da wasu jami’an tsaro uku da aka kama da laifin asabtar da wani dalibin da suka kama a zanga zanga.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00


XS
SM
MD
LG