Cira kwallo da Danny Ings ya yi a kan golan “The Reds” Alisson, bayan bugun tazarar da James Prowse ya dauko, shine ya fada raga ya kai Southampton ga yin nasara a kan tsohuwar kungiyarsa.
Liverpool da Jurgen Klopp ke horar da ita, wannan shi ne karo na biyu da ta sha kashi a wannan kakar wasa, amma kuma tana ci gaba da darewa a kan kungiyoyin Firimiya Lig da ratar kwallaye kana maki biyu kacal ne kawai ta samu a cikin maki tara a baya.
Su ko Manchester United da Manchester City duk wanda zai yi nasara a wasanninsu da suka rage, za su kara cira gwarazan na yanzu ne.
Nasarar farko da Southampton ta yi a cikin wasannin Firimiya lig biyar ya kai ta ga matsayi na shida a cikin jerin kungiyoyin wasan.
Ko shakka babu masu masaukin bakin sun taka leda kana suka saka kwallo a farkon wasan, lamarin da ba saban ba ne ga Liverpool kana suka rike dan wasan tsakiyar “The Reds” Jordan Henderson kuma suka tsare gida yayin da bakin nasu ke dannawa a gidansu.
Karin bayani akan: Liverpool, Manchester United, Manchester City, da Premier League.